Game da bisharar Markus

Bisharar Markus ita ce mafi tsohuwar rubuce-rubuce na Yesu na Nazaret, wanda aka rubuta kusan 65 AD ta hanyar abokin kusa na Yesu da almajiransa, Bitrus. Mark wani ɓangare ne na Littafi Mai Tsarki - littafi na biyu na Sabon Alkawari. Surori na 16 masu cike da ayyuka sun bayyana ainihi na musamman, koyarwa da ayyukan Yesu. Bishara yana nufin 'kyakkyawan labari', kuma Markus ya bayyana wannan littafin a matsayin “labari mai kyau game da Yesu Almasihu”.

Menene Bishara?

Mai Tsarki Mai Tsarki yana koya mana cewa dukkan mutane sun cancanci kunya da hukunci saboda zunubinmu. Amma labari mai dadi shine cewa Yesu ya mutu a kan gicciye kuma ya ɗauki hukuncin da muka cancanci. Ya tashi daga matattu a rana ta uku don tabbatar da cewa ya biya zunubin duk wanda ya amince da shi. Kuma lokacin da muka amince da Yesu a matsayin Ubangiji da Mai Ceto, Allah Ya gafarta mana cikakke kuma har abada. Muna fuskantar ainihin dangantaka da Allah wanda ba zai taɓa ƙarewa ba.

Nasihu don karatu

Kuna iya bincika wannan littafin ta babi da lambobin aya (duba hanyoyin haɗin da ke ƙasan shafin don canza babi). Misali, 'Mark 8:29' yana nufin Markus babi na 8, aya 29. Saboda Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne daga wani wuri, akwai abubuwa da yawa da za ku iya wahalar fahimta da farko. Lokacin da wannan ya faru, yi addu'a don taimakon Allah, kuma yi la'akari da karanta littafin tare da gogaggen mai bin Yesu. Sharhin kan layi kamar bibleref.com kuma na iya taimaka muku yayin da kuke karatu.

Markus

Markus 11

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
1Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, 2ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan. 3In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”
4Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, 5sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?” 6Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. 7Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. 8Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,
“Hosanna!”
“Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
10“Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!”
“Hosanna a can cikin samaniya!”
11Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
12Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. 13Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da ’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ’ya’yan ɓaure ba ne. 14Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin ’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
15Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, 16ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. 17Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’”
18Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19Da yamma ta yi, sai Yesu da almajiransa suka bar garin.
20Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!”
22Yesu ya amsa ya ce, “Ku gaskata da Allah. 23Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. 25A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
27Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. 28Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 30Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
31Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 32In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”
33Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”
Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

Ina za ku so ku je gaba?