Game da bisharar Markus

Bisharar Markus ita ce mafi tsohuwar rubuce-rubuce na Yesu na Nazaret, wanda aka rubuta kusan 65 AD ta hanyar abokin kusa na Yesu da almajiransa, Bitrus. Mark wani ɓangare ne na Littafi Mai Tsarki - littafi na biyu na Sabon Alkawari. Surori na 16 masu cike da ayyuka sun bayyana ainihi na musamman, koyarwa da ayyukan Yesu. Bishara yana nufin 'kyakkyawan labari', kuma Markus ya bayyana wannan littafin a matsayin “labari mai kyau game da Yesu Almasihu”.

Menene Bishara?

Mai Tsarki Mai Tsarki yana koya mana cewa dukkan mutane sun cancanci kunya da hukunci saboda zunubinmu. Amma labari mai dadi shine cewa Yesu ya mutu a kan gicciye kuma ya ɗauki hukuncin da muka cancanci. Ya tashi daga matattu a rana ta uku don tabbatar da cewa ya biya zunubin duk wanda ya amince da shi. Kuma lokacin da muka amince da Yesu a matsayin Ubangiji da Mai Ceto, Allah Ya gafarta mana cikakke kuma har abada. Muna fuskantar ainihin dangantaka da Allah wanda ba zai taɓa ƙarewa ba.

Nasihu don karatu

Kuna iya bincika wannan littafin ta babi da lambobin aya (duba hanyoyin haɗin da ke ƙasan shafin don canza babi). Misali, 'Mark 8:29' yana nufin Markus babi na 8, aya 29. Saboda Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne daga wani wuri, akwai abubuwa da yawa da za ku iya wahalar fahimta da farko. Lokacin da wannan ya faru, yi addu'a don taimakon Allah, kuma yi la'akari da karanta littafin tare da gogaggen mai bin Yesu. Sharhin kan layi kamar bibleref.com kuma na iya taimaka muku yayin da kuke karatu.

Markus

Markus 7

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
1Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu. 2Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta, wato, da ba a wanke ba. 3(Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda al’adun dattawa suka ce. 4Sa’ad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu al’adu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci.)
5Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin al’adun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa marasa tsabta?”
6Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,
“ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,
amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7 A banza suke mini sujada,
koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’
8 Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”
9Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku! 10Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’ 11Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah), 12sa’an nan haka ba kwa ƙara barinsa yă yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu. 13Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin al’adun da kuke miƙa wa ’ya’yanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”
14Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan. 15Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”
17Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 18Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. 19Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, sa’an nan kuma yă fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)
20Ya ci gaba, “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi. 21Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina, 22kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta. 23Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”
24Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yă sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. 25Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. 26Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta.
27Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”
28Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.”
29Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”
30Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
31Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis. 32A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin.
33Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”). 35Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.
36Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. 37Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”

Ina za ku so ku je gaba?