Game da bisharar Markus

Bisharar Markus ita ce mafi tsohuwar rubuce-rubuce na Yesu na Nazaret, wanda aka rubuta kusan 65 AD ta hanyar abokin kusa na Yesu da almajiransa, Bitrus. Mark wani ɓangare ne na Littafi Mai Tsarki - littafi na biyu na Sabon Alkawari. Surori na 16 masu cike da ayyuka sun bayyana ainihi na musamman, koyarwa da ayyukan Yesu. Bishara yana nufin 'kyakkyawan labari', kuma Markus ya bayyana wannan littafin a matsayin “labari mai kyau game da Yesu Almasihu”.

Menene Bishara?

Mai Tsarki Mai Tsarki yana koya mana cewa dukkan mutane sun cancanci kunya da hukunci saboda zunubinmu. Amma labari mai dadi shine cewa Yesu ya mutu a kan gicciye kuma ya ɗauki hukuncin da muka cancanci. Ya tashi daga matattu a rana ta uku don tabbatar da cewa ya biya zunubin duk wanda ya amince da shi. Kuma lokacin da muka amince da Yesu a matsayin Ubangiji da Mai Ceto, Allah Ya gafarta mana cikakke kuma har abada. Muna fuskantar ainihin dangantaka da Allah wanda ba zai taɓa ƙarewa ba.

Nasihu don karatu

Kuna iya bincika wannan littafin ta babi da lambobin aya (duba hanyoyin haɗin da ke ƙasan shafin don canza babi). Misali, 'Mark 8:29' yana nufin Markus babi na 8, aya 29. Saboda Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne daga wani wuri, akwai abubuwa da yawa da za ku iya wahalar fahimta da farko. Lokacin da wannan ya faru, yi addu'a don taimakon Allah, kuma yi la'akari da karanta littafin tare da gogaggen mai bin Yesu. Sharhin kan layi kamar bibleref.com kuma na iya taimaka muku yayin da kuke karatu.

Markus

Markus 8

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
1A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa ya ce, 2“Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci. 3In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”
4Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”
5Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?”
Suka ce, “Bakwai.”
6Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka. 7Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. 8Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. 9Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su, 10sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.
11Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yă nuna musu wata alama daga sama. 12Sai ya ja numfashi mai zurfi ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.” 13Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.
14Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan. 15Yesu ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”
16Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”
17Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne? 18Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba? 19Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?”
Suka amsa, “Sha biyu.”
20 “Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?”
Suka ce, “Bakwai.”
21Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”
22Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. 23Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”
24Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”
25Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai. 26Yesu ya sallame shi gida ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen.”
27Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”
28Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Iliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.”
29Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?”
Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.”
30Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.
31Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi. 32Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsawata masa.
33Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da al’amuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”
34Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni. 35Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. 36Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? 37Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? 38Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”

Ina za ku so ku je gaba?